Labarai
Kotu Ta Tsare Mutumin Da Ya Yi Yunkurin Kashe Kansa A Wurin ‘Yan Sanda
Wata babbar kotun majistare a jihar Ondo da ke zamanta a garin Odigbo a karamar hukumar Odigbo ta jihar, ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai suna Kayode Ojo a gidan yari.
Umarnin tsare mutumin ya biyo bayan samunsa da laifin yunkurin kashe kansa a cikin dakin da ‘yan sanda suke tsare wadanda ake zargin masu laifi ne (Cell).
Tun da farko jami’an rundunar ‘yan sandan jihar sun kama wanda ake tuhuma, saboda yunkurin kashe kansa.
Ana zarginsa ne da yunkurin shan wani abu mai guba a cikin dakin masu laifi.
A cewar mai gabatar da kara na ‘yan sandan, Mista James Usifo, laifin ya saba wa sashe na 327 na kundin Code Cap. 37 Juzu’i na 1 Dokokin Jihar Ondo ta Najeriya, na 2006.
Usifo ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin yunkurin kashe kansa ta hanyar shan wani abu mai guba da ake zargin yana maganin kashe kwayoyin cuta a hannun ‘yan sanda.
Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun, D. O. Ogunfuyi, a hukuncin da ya yanke, ya bada umarnin tasa keyar wanda ake zargi zuwa gidan yari na Okitipupa tare da dage shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Oktoba, 2023, domin zartar masa hukunci.
