Labarai
‘Yan Ta’adda Ba Su Da Matsuguni A Jiharmu — Gwamnan Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce gwamnatinsa ba za ta bai wa ’yan tada kayar baya damar gudanar da ayyukansu a jihar ba.
Gwamnan yana mai tabbatar da aniyar gwamnatinsa na sake dawo da amanar da daukacin al’umma suke da ita akan jihar.
A cikin sakon sa n Mauludi, a Laraba, Gwamna Sani yace Ina yiwa al’ummar Musulmin Najeriya da Jihar Kaduna barka da wannan rana. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ni’imominsa da kariyarsa da shiriyarsa a gare mu.
“Wannan shi ne bikin Maulud na farko tun bayan da muka dare karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Mun zauna kan harkokin mulki. Mun sadaukar da kanmu don sake gina zaman lafiyar al’ummominmu da ya lalace da rarrabuwar kawuna.
“Jama’ar mu sun cancanci zaman lafiya da muhalli mai nutsuwa ta yadda za su sake gina rayuwarsu da kuma ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin jiharmu mai daraja.
“Bukin Maulud na bana wata dama ce ga ’yan jihar da za su yi koyi da kyawawan dabi’un Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) domin warkar da al’ummarmu da sake gina tattalin arzikinmu da ya lalace”.
Annabinmu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsaya kan soyayya, juriya, hakuri, adalci, da gafara. Ya fuskanci tsanantawa saboda imaninsa. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da walwala da tsaron al’ummarsa duk da irin jarabawar da ya fuskanta.
Dole ne a matsayinmu na mutane, mu ƙulla niyyar sanya abubuwan da ba su da daɗi a baya. Mu samarwa junanmu zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, za mu iya warware bambance-bambancenmu da sake gina zaman lafiya da aminci ga al’ummominmu.
Kiyayya, rashin yarda da zato sun sabawa ci gaba ya kamata mu hana ‘yan tada kayar baya mazauni a yankunanmu.
Gwamnatinmu za ta ci gaba da karfafa tattaunawa tsakanin addinai za mu baiwa hukumar zaman lafiya ta jihar Kaduna duk wani goyon baya da take bukata domin magance rikice-rikicen da aka dade ana fama da su da kuma samun fahimtar juna a tsakanin al’ummarmu.
