Labarai
Kano: Hukumar Kula Da Asibitoci Ta Rufe Wani Asibitin Bisa Rashin Bin Ka’idojin Aiki
Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe asibitin Reach saboda rashin bin dokar da ta kafa hukumar da ka’idojin aiki.
Babban Daraktan hukumar Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad ne ya bayyana haka jim kadan bayan rufe asibitin tare da ma’aikatan hukumar.
Ya ce asibitin yana kan titin kotu, a unguwar Gyadi-Gyadi a cikin birnin Kano, ya kara da cewa an rufe shi ne saboda an bude shi kafin a kammala takardu da ka’idojin da PHIMA ta shimfida, wadanda suka dace don bude kowace cibiyar kula lafiya mai zaman kanta.
KARANTA LABARIN Jami’an DSS Sun Kama Matashiyar Da Yi Wa Shattima, Gawuna Barazana
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya sanyawa hannu ranar Litinin.
Sanarwar ta ce shugaban ya bayyana cewa bayanan da asibitin ya gabatar wa hukumar sun sabawa bayanan da suke da shi dangane da asibitin a lokacin da aka gayyace su domin tattaunawa.
Ya yi takaicin yadda ma’aikatan suka sanya sunan asibitin Reach Clinic da aka mika wa PHIMA saboda ma’aikatan da suka yi rajista ba ma a jihar sukw ba. Ta yadda wasu ba sa aiki da asibitin.
“Abin takaici, likitocin da muka hadu da su suna aiki a lokacin da muka isa asibitin ba su ne aka ba mu sunayensu ba. Dangane da haka, muna ganin ya dace a rufe asibitin har sai sun bi duk ka’idoji da dokokin aiki, domin ba a ma ba su izinin fara aiki ba,” in ji Farfesa Salisu.
Ya kara da cewa, dokar hukumar PHIMA da ta ba ta ikon kula da harkokin cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta tanadi cewa duk wata cibiya da za a bude, dole ne ta zo hukumar domin cike takardun da ake bukata dangane da ma’aikatanta da ayyukan da za ta aiwatar.
Jaridar Blueprint ta rawaito cewa DG ya kara da cewa da duk wadannan, ba za a bar irin wannan cibiya ta fara aiki ba har sai lokacin da hukumar ta je ta duba tare da tantance bayanan da aka mika musu sannan ta gamsu.
“Reach Clinic kawai ya buɗe asibitin ba tare da izininmu ba duk da kura-kurai da suke da su. Shi ya sa muka rufe asibitin. Zai kasance a rufe har sai an bamu sahihan bayanan da muke bukata kuma muka gamsu da su,” in ji Farfesa Salisu.

Pingback: Neja: Akalla Gawarwaki 6 Aka Gano Cikin Mutane 22 Da Suka Nutse A Hatsarin Kwale-kwale - KAKAKI HAUSA