Connect with us

Labarai

Neja: Akalla Gawarwaki 6 Aka Gano Cikin Mutane 22 Da Suka Nutse A Hatsarin Kwale-kwale

Akalla fasinjoji 22 ne suka nutse a ranar Litinin a wani hatsarin jirgin kwale-kwale a jihar Neja.

An ce wadanda abin ya rutsa da su sun taso ne daga kauyen Kasabu da ke karamar hukumar Agwara ta jihar Neja zuwa Yauri a jihar Kebbi, a safiyar ranar Litinin din ne jirgin ya kife saboda iska mai karfi da ta taso.

Ya zuwa daren ranar Talata, tawagar bincike da ceto ta gano gawarwaki shida ne kawai, ciki har da na wani Fasto a Kebbi da ke zaune a jihar Neja.

KARANTA LABARIN Hukumar PHIMA Ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kano A Kano

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, yawancin wadanda abin ya shafa sun je cin kasuwa ne a kasuwar Litinin da ke garin Yauri a jihar Kebbi a lokacin da lamarin ya faru.

Kakakin hukumar NSEMA, Hussaine Ibrahim, ya ce ana kyautata zaton yawancin wadanda ya rutsa da su ba sa sanya rigar ceto ba.

“Mun samu rahoto daga jami’an ofishinmu dake Agwara kan lamarin hatsarin kwale-kwalen da ya afku a ranar Litinin tsakanin karfe 11 na safe da 12 na rana.

“Tun da safe, an yi ruwan sama mai tsanani a wurin, kuma hakan ya yi wa tawagar masu aikin ceto wahala wajen samun sakamako mai yawa.

“Sun kasance a cikin ruwa tun da safe; ruwan sama ya sa al’amura sun yi wahala. Mutanenmu da ke wajen sun ce sun sake gano wasu gawarwaki a yau.

“Tun da safe suke kan ruwa amma ruwan sama ya hana aikin. A safiyar yau ne suka gano gawarwaki guda hudu sannan kuma da yammacin yau sun samu guda biyu. Wadanda abin ya shafa ‘yan jihar Neja ne amma daya daga cikin su dan asalin Zuru ne a jihar Kebbi,” inji Ibrahim.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Kebbi: NIWA Ta Tabbatar Da Ceto Mutane 14 Da Rai A Hatsarin Kwale-kwale - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet