Labarai
Kebbi: NIWA Ta Tabbatar Da Ceto Mutane 14 Da Rai A Hatsarin Kwale-kwale
Hukumar kula da yanayin ruwa ta kasa NIWA ta ce, a ranar Laraba, an ceto mutane 14 daga cikin fasinjoji 22 da ke cikin wani jirgin ruwa da ya kife a tsakanin jihohin Kebbi da Neja.
NIWA, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta ce an gano gawarwakin wasu fasinjoji shida, inda ta kara da cewa ana ci gaba da neman sauran fasinjojin.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata, wanda ya shafi wani jirgin ruwa daga Kauyen Kasabo da ke karamar hukumar Agwara ta jihar Neja ya nufi kasuwar Yauri a jihar Kebbi.
NIWA ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa matukin jirgin ya yi biris da yanayin da ake ciki.
“Bincike na farko daga ofishin mu da ke garin Yauri a jihar Kebbi ya nuna cewa kwale-kwalen katako ne ya kife ne a sakamakon wata iska mai karfi da ta biyo bayan rashin kyawun yanayi.
“Abin bakin ciki ne abin da za a iya gujewa farursa saboda kuskuren ɗan adam kuma matuƙin jirgin ruwa ya yi watsi da yanayin da ake ciki.
“Lokacin da ma’aikacin jirgin ya kamata ya sauka a gabar bakin kogin mafi kusa, wato kiyaye ka’idojin yanayi da NIMA take fadakarwa, sai ya yanke shawarar ci gaba da tafiya, wanda hakan ya sa fasinjojin suka firgita, wasun su kuma ba su iya tsallake rijiya da baya ko sanya rigar ceto ba. daga baya jirgin ya kife,” in ji NIWA.
KARANTA LABARIN Gawarwaki 6 Aka Gano Cikin Mutane 22 Da Suka Kife Da Kwale-kwale A Neja
Ya kara da cewa “An ceto mutane 14 da ransu sannan kuma an dauko gawarwaki shida yayin da ake ci gaba da neman sauran gawarwakin biyu.”
A halin da ake ciki, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, a ranar Laraba, ta fitar da sunaye da hotunan wasu gawarwakin wadanda jirgin ya kife da su.
Kakakin hukumar ta NSEMA, Hussaine Ibrahim, wanda ya zanta da The PUNCH ta wayar tarho, ya ce biyu daga cikin wadanda suka mutu, Murna Ezekiel da Amos Samuel, sun fito ne daga jihar Kebbi yayin da sauran hudun, Bilyaminu Kontagora, Dauda Alhassan Kasabu, Iliya Kpchra Busuru da Joshua Auta sun fito ne daga jihar Neja.
Ibrahim ya kuma bayyana cewa an sake gano wasu gawarwaki biyu a safiyar Laraba amma ana kokarin gane su.

Pingback: Yara Dalibai 60 Aka Kwantar A Asibiti Sakamakon Shan Alewar Da Aka Yi Da Wiwi - KAKAKI HAUSA