Connect with us

Addini

Yadda Aka Yi Cikar Kwari A Kano Yayin Da Ake Bikin Takutaha

Jama’a sun taru a birnin Kano domin gudanar da bukukuwan Takutaha, domin ta juna barka da Maulidin Manzon Allah (SAW).

Ranar 12 ga watan Rabi’u Awwal a shekarar giwa, wato wata na uku a kalandar Musulunci, ita ce ranar maulidin Manzon Allah (SAW). Don haka ne ake bikin ranar 19 ga wannan wata a matsayin ranar radin suna.

Wannan ita ce ranar da al’ummar Kano suke bikin Takutaha.

Ku tuna cewa gwamnatin jihar ta ayyana ranar Larabar a matsayin ranar hutu domin bikin.

KARANTA LABARIN Majalisar Dattijai Ta Tantance Mutane Ukun Da Tinubu Ya Aika Mata

Wakilinmu Nura Ahmad Hassan a hirarsa da Sharu Sani Janbulo ya bayyana cewa an kwashe sama da shekaru 20 ana gudanar da taron.

Ya ce, “A yau mun fito ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabinmu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

“Mun shafe kwanaki uku a Janbulo muna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi, kuma yau kwana na hudu kenan shi ne muke Takutaha”.

Ya ce bikin kuma lokaci ne da musulmi za su nuna koyarwar Manzon Allah (SAW) da kuma kara sanin rayuwarsa.

Ya kara da cewa makasudin gudanar da bikin shi ne kuma nuna soyayya, jin dadi da ziyartar abokai da ‘yan uwa.

An fara bikin ne da jerin gwano daga Janbulo zuwa Tal’udu zuwa Mandawari a cikin babban birnin Kano.

Tattakin ya cika da jama’a daga jihohi daban-daban da suka zo Kano domin nuna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi.

Umar Abubakar daga jihar Binuwai ya ce ya zo Kano ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi.

Ya shawarci mutane da su bi tafarkin Annabi.

Abdulkadir Zubair na Rijiyar Zaki ya bayyana farin cikinsa tare da addu’ar Allah ya kara hada kan al’ummar musulmi.

Bikin dai ya kunshi karatuttukan Alkur’ani mai girma da kuma fadin Manzon Allah (Hadisi), da sanya sabbin tufafi (musamman na yara).

Haka kuma bukukuwan sun hada da ayyukan addini kamar lakcoci da wa’azi da yabo ga manzon Allah mai tsira da amincin Allah.

Ga wani rukunin jama’a kuma, kololuwar taron Takutaha shi ne babban taron jama’a a saman tsaunin Dala inda suke cin abinci tare da kallon wasu abubuwan nishadantarwa da na addini.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet