Lafiya
Yara Dalibai 60 Aka Kwantar A Asibiti Sakamakon Shan Alewar Da Aka Yi Da Wiwi
Sama da yara Dalibai 60 a Jamaica an garzaya da su asibiti a ranar Laraba bayan sun sha alewar da aka cakuda da tabar wiwi, in ji ministan ilimi na kasar.
Ministar Matasa ta Ƙasa, Fayval Williams ta rubuta a shafinta na X cewa ɗaliban firamare sun fito ne daga St. Ann’s Bay, kimanin kilomita 80 daga Kingston, babban birnin ƙasar.
Ta ce wasu daga cikin yaran suna ta amai da fuffuka, ta kara da cewa babu wani yaro da aka ruwaito yana cikin wani hali mai tsanani.
“Likitoci da ma’aikatan jinya suna yin duk abin da za su iya don tabbatar da cewa daliban sun murmure,” in ji Williams.
Ana kyautata zaton yaran ‘yan tsakanin shekaru 12 zuwa kasa ne lamarin ya shafa.
KARANTA LABARIN An Ceto Mutane 14 A Raye Da Gawarwaki 6 Cikin 22 Da Suka Yi Hatsarin Kwale-kwale A Neja
Shugaban makarantar firamaren ta Ocho Rios ya shaida wa Jamaica Observer cewa “mai siyar da alewar ya sayar da alewar ga daliban.”
Shugaban ‘yan sandan St. Ann Dwight Powell ya bukaci duk wanda ke da bayanai game da mai siyar da alewar ya tuntubi hukumomin tsaro mafi kusa.
Fakitin ya bayyana cewa samfurin ya ƙunshi Delta-8 tetrahydrocannabinol (THC), wani abu na psychoactive da aka samu a cikin tabar, wanda ya haɗa da marijuana da nau’in hemp.
Yana da “tasirin tunani da sa maye,” a cewar Hukumar kula da abinci da Magunguna ta Amurka (FDA).
Ministar ta kuma hada da hoton kunshin alewar da ke nuna gargadin gwamnati a baya tana mai cewa “a kare yaran da ba za su sha ba” da kuma “ba wanda ya kai shekara 21 ya yi amfani da shi.”
Fakitin ya nuna cewa samfurin bai samu amincewar FDA ba.
Jamaica ta haramta cannabis ga mutanen da basu haura shekaru 18 ba a 2015, tare da mallakar oza 2 (gram 56) ko ya zama ƙaramin laifi.

Pingback: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Karin Mutane Uku Don Nada Su Ministoci - KAKAKI HAUSA