Labarai
INEC Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Janyewa Daga Daukaka Karar Shari’ar Zaben Kano
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta janye takardar janyewa daga daukaka karar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano.
Wannan na zuwa ne bayan ta tura wasikar janyewar da minti 40 kamar yadda shugaban sashin kula da shari’a na hukumar zabe a Kano Sulaiman Alkali ya bayyana wa manema labarai a ranar Asabar din nan.
Jaridar KakakiHausa ta rawaito cewa Hukumar zabe (INEC) ta ce ta janye karar da ta shigar a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.
Jaridar Daily Post, ta samu labarin a ranar Asabar din nan cewa INEC ta janye wasikar ta, ta farko da ke nuna janyewa daga daukaka karar da kotun ta yanke.
A wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, Suleiman Alkali, a ranar Juma’a, ta ce ta janye karar da ta shigar saboda ba ta da dalilin yin hakan.
Wasikar, wacce aka aike wa sakataren kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano, a wani bangare tana cewa: “Shedikwatar hukumar ta umarce ni da cewa in sanar da ku, INEC ba ta da dalilin daukaka kara kan duk wani hukunci.
“Saboda haka, kwamishinan shari’a na kasa da kuma kwamishinan kasa mai kula da shiyyar Kano ya ba da umarnin a janye karar kuma a mika duk wani tsari na duk wani kararraki ga ofishin a Kano.”
Sai dai Alkali ya ce an janye wasikar da aka rubuta wa kotun, nan take.
Wani jami’in gwamnati ya shaida wa manema labarai cewa a lokacin da Alkali ya tattauna da wasu lauyoyi da ke wakiltar INEC kan lamarin, ya yi ikirarin cewa an rude shi ne har ta kai ga rubuta wasikar. Ya kuma ba da uzurinsa kan “kuskurensa”.
Sai dai bai bayyana wanda ya umarce shi da aikata hakan ba. Ya ce ya janye wasikar ne cikin mintuna 40 da mika ta ga kotun, amma ya yi mamakin yadda ta shiga kafafen yada labarai.
A cewarsa, wasu manya sun so su yi anfani da shi, kuma tuni aka fargar da shi da cewa lamari ne mai matukar muhimmanci.
