Labarai
Shiri Ya Yi Nisa Don Fara Ayyukan Gadar Sama Da Kasa A Kano — Gwamnan Jihar
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin raba buhunan hatsi da kuma baiwa matasa da mata da nakasassu tallafin kudi.
A ci gaba da kokarin gwamnatinsa na bayar da tallafi ga al’ummar jihar don rage radadin tallafin man fetur, an kammala shirye-shiryen raba hatsi da suka hada da shinkafa da masara a fadin mazabu 484 da ke cikin kananan hukumomin jihar 44.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yau a wajen wani taro da shugabannin kananan hukumomin jiha da Sakatarori hudu na kwamitin (Community Re-Orientation Committee (CRC), Lafiya Jari, Kano PRO-PA da kuma Kwankwasiyya) taron da ya gudana a dakin taro na Coronation Hall, da ke gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan ya ce rabon kaso na biyun ya zama wajibi duba da irin matsalolin da mutane ke ciki sannan ya yi kira ga masu gudanar rabar a matakin jiha da kananan hukumomi da su kasance masu adalci a cikin shirin domin cimma burin rage wahalhalun da ake ciki na matsananciyar yunwa da tsananin talauci da ake ciki a halin yanzu.
Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa, shirye-shirye suna nan don karfafar bangarori ukun da zasu amfana da yawansu ya kai 4,840 a tsakanjn mata, matasa da nakasassu wadanda za a horar da su tare da samar musu da jarin fara sana’a.
“Za kuma mu tabbatar da bullo da tsarin motocin haya da motocin bas na Amana ga matasan mu, za a saka wasu masu tuka babur (Yan Adaidata Sahu) a cikin wannan shirin don inganta matsayinsu.”
A bangaren ayyukan raya kasa kuwa, gwamnan ya ce ayyukan kilomita biyar a kananan hukumomi 44 da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar a wa’adin mulkinsa na biyu, an mayar da ‘yan kwangilar wuraren domin ci gaba da gudanar da ayyukan da kuma kammala su kamar yadda aka tsara.
Haka kuma a yayin taron ya sanar da shirin gwamnatin jihar na shirya wani gidauniyar roko ga jami’an tsaro da ke aiki a jihar ta yadda za a samar musu da kayan aikin wanzar da zaman lafiya.
Alh Abba Kabir ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana wasu tsare-tsare na raya kasa a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, fadada tituna a cikin birnin Kano, gina gada da kuma hanyoyin karkashin kasa domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa, kawar da madatsun ruwa, gyare-gyaren asibitoci da makarantu a kananan hukumomi 44 na Kano.
Gwamnan ya yaba da irin goyon baya da hadin kai da al’ummar Kano suke baiwa gwamnatin sa, sannan ya bukaci da a dawwama da addu’a a wannan lokaci domin ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
