Connect with us

Labarai

FG Ta Tabbatar Wa Da ‘Yan Najeriya Cewa Radadin Cire Tallafin Mai Na Dan Lokaci Ne

 

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa radadin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sanadin cire tallafin man fetur na wani dan lokaci ne.

Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Mohammed Idris ya ba da wannan tabbacin a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa a Abuja.

Ya bayyana cewa a fili yake cewa babbar fa’idar cire tallafin man fetur talaka ne zai amfana.

Idris ya ce abin takaici ne a ce mutane kalilan ne kawai ke cin gajiyar tsarin tallafin, inda ya kara da cewa ‘yan kadan ne ke cin moriyar dukiyar kasa baki daya ta hanyar cin gajiyar mafi yawansu.

“Don haka, Shugaba Bola Tinubu ya ce ba zai aminta da hakan ba. Ya tsaya tare da mafi yawan ’yan Najeriya.

“Ko da yake cirewar zai kasance mai zafi a farkon, zai kasance mafi kyau ga dukkan mu a karshen,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa: “Cire tallafin man fetur kamar mai juna biyu ce lokacin nakuda da za ra haihu; lokacin da take cikin zafin nakuda, za ta ji kuma ta fi son ba ta samu damar haihuwa ba.

“Ina tsammanin, ana iya amfani da wannan kwatancen ga wannan batu na cire tallafin man fetur.

“Don haka, zafin zai zama na ɗan lokaci, amma a ƙarshe, za mu fi dacewa da shi; abin da Shugaba Bola Tinubu ya yi imani da shi ke nan, kuma abin da yake nudarwa ke nan”.

Ministan ya tuna cewa a cikin ‘yan watannin farko na gwamnatin Tinubu ya ware kudade ga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya domin a samu saukin matsalar cire tallafin.

“Wannan shi ne saboda Tinubu ya yi imanin cewa gwamnonin jihohi mutane ne da suka san yankunansu sosai.

“Ya kuma samar da hatsi iri-iri da takin zamani don taimakawa rage damuwar da ‘yan Najeriya ke damun kai game da cire tallafin man fetur.

“Ina tabbatar muku da cewa nan gaba kadan Najeriya za ta fi dacewa da ita,” in ji Idris

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet