Labarai
Kotu Ta Yanke Hukunci Zaman Gidan Yari Ga Wanj Mutum Bayan Kusan Shekaru 11 Ana Gudanar Da Shari’a
Wata kotun majistare da ke zamanta a Igbosere a yankin Tinubu a ranar Juma’a ta yanke wa wani mutum mai suna Dayo Bakare mai shekaru 38 hukuncin daurin shekaru 34 a gidan yari bisa samunsa da laifin yin garkuwa da wata mata ‘yar shekara 27 da haihuwa a shekarar 2012.
Alkalin kotun, Adetokunbo Omoyele, ta yanke wa Bakare hukuncin ne bayan ta same shi da laifukan da ‘yan sanda suke tuhumarsa da shi.
An gurfanar da wanda ake tuhumar ne a ranar 17 ga Nuwambar 2012, bisa laifin hada baki, jima’i ba da son rai ba, tsarewa, garkuwa da mutane, farmaki, da kuma mummunar illa.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Cyriacus Osuji, ya shaida wa kotun cewa Bakare ya hada baki da wasu mutane domin yi wa matar fyade.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Janairu, 2012, da misalin karfe 4 na yamma a wani gida da ke kan titin Akeem Lasisi, a unguwar Shasha a jihar Legas.
Osuji ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya yi lalata da matar ba bisa son ranta ba kuma ya tsare ta tsawon sa’o’i takwas.
Ya lura cewa Bakare ya kuma yi wa wadda lamarin ya shafa karaya.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun ci karo da sashi na 411, 258, 144 (b), 269 (b) (1), 17, da 171 na dokar laifuka ta jihar Legas 2011.
Sai dai Bakare ya musanta aikata laifin.
Shekaru 11 da faruwar lamarin, Alkalin kotun, Omoyele ya same shi da laifi kuma ya yanke masa hukuncin zaman gidan dan kande
Ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin hada baki; shekaru 14 na jima’i na haram; shekaru biyar don tsare mutum da niyyar yin jima’i ba bisa ka’ida ba; shekaru 10 na garkuwa da mutane; da shekara uku saboda duka da cin zarafi.
Jaridar PUNCH ta rawaito I Alkalin kotun, Omoyele, ya ce wa’adin zaman gidan yarin zai tafi lokaci guda daga ranar da aka yanke masa hukuncin.
