Labarai
Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Shugaban INEC Da Ya Mutunta Kalaman Da Ya Yi
Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya mutunta kalaman da ya yi game da shigar da sakamakon zaben jihohin Imo, Kogi, da Bayelsa a dandalin hukumar na (IReV).
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a Abuja.
Ologunagba ya ce PDP ta lura da maganar da Yakubu ya yi cewa INEC za ta yi amfani da dandalin IReV da (BVAS) don aikawa da watsa sakamakon zabukan gwamnonin Imo, Bayelsa da Kogi.
“PDP ta lura cewa shugaban INEC ya tabbatar da yin amfani da BVAS da IREV a wannan zaben kuma ko a zaben da ya gabata ya zama wajibi ga doka.
“PDP ta dorawa Yakubu alhaki da kuma yin la’akari da furucinsa na cewa INEC zata watsa sakamakon zabe kai tsaye daga rumfunan zabe ta hanyar amfani da wadannan shafuka.
“PDP ta shirya tsaf domin gudanar da wadannan zabukan kuma bisa kudirin INEC ba za ta amince da wata hanya ta mika sakamako a wadannan zabukan ba sai dai yadda shugaban INEC ya furta daidai da dokar zabe ta 2022,” Ologunagba yace.
Ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta fara horas da wakilanta na zabe a kowane mataki domin tabbatar da bin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) dokar zabe ta 2022, jagorori da dokokin INEC, musamman kamar yadda aka tabbatar.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta ci zabe a jihohin uku.
Ya ce a Bayelsa, PDP tana da Gwamna Douye Diri, “abin al’ajabi kuma mai nuna kwarewa, wanda ke kan kasa kuma yana samun gagarumin goyon bayan jama’a.”
Ya ce a Kogi, jam’iyyar PDP tana da fitaccen dan takara, Sanata Dino Melaye wanda farin jininsa da karbuwar jama’a ya dugunzuma gaba daya tare da yin watsi da dan takarar jam’iyyar APC, Usman Ododo.
A Imo, Ologunagba ya bayyana cewa PDP na da fitaccen dan takara a Sanata Samuel Anyanwu wanda farin jininsa da karbuwarsa a fadin jihar ya jefa Gwamna Hope Uzodimma da APC a jihar cikin fargabar mutuwa.
