Labarai
Ma’aikatan KEDCO Sun Rufe Hedkwatarsu, Saboda Matsalar Biyan Kudade
Ma’aikatan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki mai kula da Kano, Jigawa, Katsina a ranar Litinin din nan sun rufe kamfanin na Kano (KEDCO).
Rufe kamfanin na zuwa n bisa zargin gaza cire musu kudaden fansho da suka yi a cikin watanni 72 da suka gabata.
Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) sun sha alwashin ci gaba da rufe kamfanin har sai an tabbatar da biyan kudaden.
Malam Ado Ririwai, Shugaban kungiyar na Arewa maso Yamma, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN cewa ma’aikatan ba za su bari a ci gaba da irin wannan hali na rashin kyautawa ba.
Riruwai ya zargi KEDCO da cin zarafin shugabannin kungiyar da ke kokarin yin magana a madadin ma’aikatan.
“Wannan aikin na mulkin mallaka ne; haƙƙin ma’aikata ne su yi yaƙi don abin da yake nasu,” inji shi.
Shugaban kungiyar ya kuma zargi kamfanin da kin bai wa ma’aikatan hakkin kula da lafiya na asali “duk da haduran da ke tattare da ayyukansu”.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Kokarin samun martanin kamfanin ya ci tura yayin da duk ma’aikata, ciki har da ma’aikatan gudanarwa, an tilasta musu ficewa daga harabar shedkwatar kamfanin.
(NAN)
