Connect with us

Labarai

Hukumar NAFDAC Ta Lalata Jabun Magunguna Daban-Daban Na Miliyoyin Kudi

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC a ranar Larabar ta lalata kayyakin magungunan jabu da kuma wadanda wa’adinsu ya kare na sama da Naira miliyan 500 a Abuja.

Da take jawabi yayin lalata kayan, Babbar Daraktar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin an mika su ne bisa radin kai ga hukumar.

Farfesa Mojisola Adeyeye
wadda ta samu wakilcin Mista Francis Ononiwu, daraktan bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, ya bayyana cewa ana gudanar da atisayen ne a duk fadin kasar nan.

Shugabar NAFDAC ta ce an lalata kayayyakin ne domin hana su sake dawowa cikin al’umma.

Adeyeye ya lasafta wasu daga cikin kayayyakin da aka lalata a matsayin magungunan da suka hada da masu jirkitar da kwakwalwa da kuma rigakafin sa maye, antihypertensive, maganin zazzabin cizon sauro, snuff na ganye da magungunan ganye, da kuma magungunan da aka kwace daga masu safarar miyagun kwayoyi.

Ta kuma zayyana kayayyakin abinci irin su taliya, man girki na kayan lambu, abubuwan sha da ba na barasa ba, ciki har da kwantena 1 da katon 40 na madarar Faurecia da ba a yi wa rijista da hukumar kwastam ta Najeriya ba (NCS) ta mika wa hukumar.

Sauran sun hada da kayan shafawa kamar su creams, lotion, pomade, da suka hada da mayukan haska fata da aka kama daga SPAS da wuraren kawatawa, sinadarai irinsu jabun maganin kwari da na’urorin likitoci.

An lalata kayayyakin da ba su da kyau da kungiyoyin masu zaman kansu (NGOs) da Association of Community Pharmacy of Nigeria (ACPN) suka mika don lalata su.

A cewar shugabar hukumar ta NAFDAC, kiyasin farashin kayayyakin da ake lalata ya kai N535, 000, 657.00.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet