Connect with us

Labarai

Hadimin Gwamnan Katsina Ya Rasa Ransa Sanadiyyar Wani Hadarin Mota A Jihar

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi rashin babban mai taimaka masa na musamman kan ilimin addinin Islama, Shamsudeen Malumfashi, a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Hadarin ya afku ne a ranar Talata a kewayen unguwar Rigachikun da ke jihar.

An kuma binne gawarsa jim kadan bayan afkuwar hatsarin a garinsu ranar Talata.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Malumfashi a majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Ibrahim; Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki, Bello Kagara; da kuma wasu daga cikin mukarraban sa sun halarci sallar jana’izar marigayin a ranar Talatar.

Radda ya kuma jagoranci tawagar ta’aziyya a ziyarar da ya kai ga iyalan marigayin.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan sa, ya kuma roki Allah ya kula da iyalansa.

Marigayin mataimakin gwamnan ya rasu ya bar mahaifinsa, Abubakar Yusuf; da mahaifiyarsa Jamila, sai mata uku; da yara hudu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet