Featured
An Kama Dalibin Jami’ar ABU Da Ake Zargi Da Yaudarar Wani Matashi, Kuma Ya Hallaka Shi
Rundunar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma NSCDC ta kama wani Dalibin Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya da ke jihar Kaduna, dalibin likitan dabbobi mai matakin aji na 500 a jihar Bauchi bisa zargin kashe wani yaro dan shekara 17 da haihuwa.
Wanda ake zargin mai suna Abdullahi Ibrahim, an ce ya yaudari matashin dalibin da ke sakandire da hotonsa tsirara tare da jan hankalinsa ya hadu da shi don aikata luwadi.
Kwamandan NSCDC na jihar Bauchi, a Ilelaboye Oyejide, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar.
Ya ce lamarin ya faru ne a garin Misau da ke karamar hukumar Misau.
Oyejide, wanda ya bayyana cewa rundunar ta samu labarin wani lamari na kisan gilla, ta ce an samu wani dalibi mai suna Umar Usman dan shekara 17 da haihuwa, mazaunin garin Misau a nannade da yadi da aka jefar da shi a hanyar Misau.
Ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin, nan take ya kafa wata tawaga ta manyan jami’an bincike domin su je Misau su gudanar da bincike don gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, Kwamandan NSCDC ya ce: “A ranar 20 ga watan Oktobar 2023, an tsinci gawar Umar Usman da ba rai a nannade da farin kyalle an jefar a hanyar Misau.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai shi babban asibitin Misau inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa. An mika gawarsa ga ’yan uwa don yi musu jana’iza.
“Bayan cikakken bincike da ‘yan sandan suka yi, an kama wani da ake zargi mai suna Abdullahi Ibrahim, dalibi mai matakin digiri 500 na likitan dabbobi a ABU Zaria.
“Mun fahimci cewa akwai tattaunawa tsakanin wanda ake zargin, Ibrahim da marigayin, Usman. A cikin hirar, mun ga inda wanda ake zargin ya yaudari marigayin da soyayyar luwadi a lokacin da ya nuna masa hotonsa tsirara.
“Lokacin da Usman ya je ya same shi ko ta yaya, an soka masa wuka a ciki, aka nade shi da farin kyalle, aka jefar da shi a inda aka same shi.”
Ya ce a yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu domin hukunta shi.
