Tsaro
CDS Ya Gargadi Duk Masu Yunkurin Kawo Cikas Ga Zaben Gwamnan Kogi, Bayelsa Da Imo
Babban Hafson tsaron Kasar nan (CDS) Manjo Janar Christopher Musa, ya gargadi masu shirin kawo cikas a zaben gwamnoni da za a gudanar ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi da su kaurace wa jihohin.
Janar Musa ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zabe (ICCES) a Abuja.
CDS ya tabbatar wa mazauna jihohin Bayelsa, Imo da Kogi cewa kada su ji tsoro.
Ya kuma yi alkawarin cewa rundunar soji za ta bayar da cikakken goyon baya ga ‘yan sanda wajen ganin an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Rundunar soji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su kasance a shirye, don hakaduk dan Najeriya, mun tabbata ya gaji da matsalar tashin hankali hakan ne yasa zamuyi kokarin kawo sauyi.
“Muna so, a karshen wannan rana, ya kamata kowane dan Najeriya ya yi alfahari da kokarin hukumomin tsaro, da farko ya zama dan Najeriya kuma ya fahimci cewa a yanzu an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
“Muna son duk wanda ya ci zaben mu ya yi farin ciki da ya yi nasara sosai ba tare da wata fargaba ba” in ji Musa.
