Featured
Ministan Tsaro Ya Bukaci Tsaffin Sojoji Su Bada Gudunmawa Don Magance Matsalar Tsaro
Karamin ministan tsaro, kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce har yanzu Najeriya na bukatar kwarewa da shawarar hafsoshin sojan da suka yi ritaya domin tunkarar matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar nan.
Matawalle ya bayyana haka ne a wata liyafar cin abincin dare na karrama babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, wanda mambobin kungiyar makarantar soji ta kasa (NDA) 38 Regular Course Welfare Association suka shirya ranar Asabar a Abuja.
Ya kara da cewa al’ummar kasa na bukatar su a matsayin kwararrun da za su yi amfani da kwarewa da gogewarsu wajen samar da mafita ga dimbin kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Gwamna Dauda Ya Bukaci Kantomomin Da Ya Nada Da Su Taimaka Wajen Kawar Da Rashin Tsaro
A cewarsa, ana sa ran a yanzu sun samu lokaci na musamman domin tunowa da kuma gabatar da shawarwarin da za su magance matsalolin ba tare da wata tangarda ba.
“Ina so in tabbatar muku cewa ma’aikatar tsaro a shirye take ta karbe ku a matsayin kungiyar kwararrun masana don tattaunawa kan batutuwan tsaro a kasarmu.
“Saboda dimbin horo da gogewar wadannan fitattun mutane jami’an tsaro za mu tabbatar da cewa munci gaba da daukar nauyin ku a matsayin mashawartanmu a ma’aikatar tsaro” inji shi.
