Labarai
Gwamnatin Tarayya Za Ta Hada Kai Da AFRO Don Magance Matsalar Shan Taba Sigari A Najeriya
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na magance shan taba sigari a tsakanin matasan Najeriya.
Dr Jamila Ibrahim, ministar matasa ce ta bayyana haka a Abuja ranar Juma’a lokacin da Ms Bintou Camara, Daraktar Yaki da shan tabar sigari (AFRO) ta kai mata ziyarar ban girma a ofishinta.
Jamila Ibrahim ta ce shan taba a tsakanin yara babban kalubale ne da kasar ke fuskanta, wanda hakan zai iya kawo cikas ga cigaban su.
Ministar ta ce Najeriya na bukatar hada kai da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan ‘yan Najeriya su fahimci illar da shan taba sigari ke haifarwa a tsakanin matasa.
Za mu mai da hankali kan lafiyar matasa. Wannan bangare ne da ya kamata mu himmatu wajen samar da hanyoyin da za a cimma hanyar rigakafin shan taba a tsakanin yara.
Dole ne mu yi aiki tare da dokar hana shan taba a wuraren da jama’a ke taruwa musamman don hana shan taba in ji ta.
Da take magana, Camara ta ce kungiyar ta zo kasar ne domin wayar da kan ‘yan Nijeriya kan illar shan taba sigari.
“Mu ne manyan kungiyoyin bayar da shawarwari a duniya da ke ba da shawara kan shan taba sigari.
“Taba sigari ita ce kan gaba wajen haddasa mace-mace shi ya sa yake da muhimmanci mu magance shan taba” in ji ta.
Camara ta ce yana da matukar muhimmanci a magance matsalar shan sigari saboda duniya na fuskantar barazanar shan taba da ka iya shafar lafiyar jama’a.
Ta ce kungiyar ta kwashe sama da shekaru 25 tana aikin wayar da kan matasa kan illolin shan tabar ta sigari.
