Featured
Gwamnatin Kano ta Bayyana Dalilanta na Ciyo Bashin Naira Miliyan Dubu 4
Gwamnatin jihar Kano tace za ta ciyo bashin Naira Miliyan dubu huɗu domin gudanar da aikin samar da wutar lantarki a fadin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aikewa Majalisar dokokin jihar Kano, inda ya bukaci majalisar ta sahale masa ya ciyo bashin.
Gwamnatin tace idan har Majalisar ta amince da ciyo bashin to zata yi amfani da kudin ne don gudanar da aikin samar da wutar lantarki.
Da yake yiwa Majalisar karin haske, shugaban masu rinjaye na Majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala Lawan Hussaini Chediyar yan gurasa, ya ce bashin zai taimaka wajen cigaban Kano.
Lawan Hussaini ya kuma roƙi sauran yan Majalisar da su haɗa kai domin amincewa gwamnatin don ta ciyo bashin.
