Featured
IGP Ya Bukaci Likitoci Da Su Rika Bada Kulawar Gaggawa Ba Tare Da Rahoton ‘Yan Sanda Ba
Babban sufeto janar na ‘yan sandan Kasar nan, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi kira ga likitocin Najeriya da su bayar da kulawar gaggawa ga duk wadanda suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga da hatsari, ba tare da la’akari da rashin rahoton ‘yan sanda ba.
IGP ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi.
Egbetokun wanda ya bayar da umarnin aiwatar da cikakkiyar doka ta 2017 ya ce matakin ya mayar da martani ne ga korafe-korafen al’ummar Kasa suke yi dangane da munanan asarar rayuka da aka yi sakamakon rashin kula da harbin bindiga da wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Gwamnatin Kano ta Bayyana Dalilanta na Ciyo Bashin Naira Miliyan Dubu 4
Ya ce dokar ta yi daidai da aiwatar da dokar tilasta jinya da kuma kula da wadanda aka kashe a harin bindiga na shekarar 2017, wadda ta ba da umarnin cewa duk ma’aikatan kiwon lafiya su ba da fifikon kulawar gaggawa da daidaita irin wadannan majinyata, tare da sanin mahimmancin kulawar likitocin akan lokaci.
Wannan yana nuna matsayi da alhakin likitocin masu kula da kiwon lafiya don tabbatar da kula ta rayuwa da kuma ceton rai ga masu bukatar taimakon gaggawa da nufin cike gibin da ke tsakanin hukumomi.
