Connect with us

Featured

Rashin Ingantaccen Fansho Ne Ke Ragewa Jami’anmu Kwarin Gwiwa – IGP

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana damuwa kan halin da tsofaffin jami’an ‘yan sanda ke ciki karkashin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS), yana mai cewa da yawa daga cikinsu suna rayuwa cikin kaskanci da wulakanci.

Ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da manyan jami’an rundunar a birnin Abuja, inda ya jaddada cewa wahalar da tsofaffin jami’an ke fuskanta na sanya fargaba da rashin kwarin gwiwa a tsakanin jami’an da ke aiki a halin yanzu.

A ranar 21 ga Yuli, 2025, wasu tsofaffin ‘yan sanda sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, suna korafi kan yadda ake musu rashin adalci da kuma ƙarancin kudin fansho da ake biyansu, tare da bukatar a cire su daga tsarin CPS.

IGP Egbetokun ya ce: “Yau da kullum, mafi yawan tsofaffin jami’an ‘yan sanda na rayuwa cikin hali mai muni da rashin kima, la’akari da gudummawar da suka bawa ƙasa. Fanshon da ake biyansu kadan ne ƙwarai kuma ba ya wadatar da su ko don biyan bukatu na yau da kullum – lafiya, matsuguni ko rayuwa mai mutunci.”

Ya kara da cewa, “Ina jajircewa matuka wajen ganin an kyautata walwala da jin daɗin tsofaffin jami’anmu karkashin CPS. Rayuwar da suke ciki bayan ritaya abin tausayi ne, kuma ba za a yarda da haka ba. Wannan matsin rayuwa yana kara haddasa fargaba a zukatan masu aiki yanzu, inda suke ganin ritaya tamkar faduwa ce cikin wahala.”

IGP din ya ce wannan yanayin yana rage kwarin gwiwar jami’an da ke bakin aiki.

“Yanzu haka, akwai yawaitar fargaba a tsakanin ma’aikata masu aiki – fargabar cewa ritaya tamkar fadawa ne cikin wahala. Wannan ra’ayi ya yi wa jami’ai katutu har yana rage musu kwarin guiwa.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet