Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kawo Ƙarshen Yajin Aikin jami’o’i A Najeriya

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar kawo karshen yajin aikin da ya dabaibaye manyan makarantu a Najeriya, inda ya ce za a kara kyautata mu’amala da cika yarjejeniyoyi da kungiyoyin malamai.

Alausa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Channels Television a ranar Talata 29 ga Yuli, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni kai tsaye cewa kada a sake samun tsaiko a harkar ilimin gaba da sakandare.

“Shugaban kasa ya bayar da umarni kai tsaye, cewa daga yanzu ba za a sake samun ASUU ko kowace kungiya ta jami’a su shiga yajin aiki ba.” In ji ministan.

Ya kuma bayar da tabbacin samun kyakkyawar alaka da kungiyoyin da kuma gaskiya daga bangaren gwamnati.

“Dole ne a gina kyakkyawar alaka da ASUU, NASU, SANU, COEASU, da dukkan kungiyoyi. Kuma fiye da haka, gwamnati na bukatar nuna niyyarta ta gari. Gwamnati tana da alhakin cika alkawuran da ta dauka,” a cewar sa.

Dangane da korafin jinkirin biyan albashi daga wasu malamai, Alausa ya bayyana cewa gwamnati ba ta daina biyan albashi ba.

“Muna biyan albashi. Muna biyan albashi akai-akai. Abin da ya faru kawai shi ne, bayan da jami’o’i suka fita daga tsarin IPPIS wanda ya tauye musu ‘yanci, Shugaban kasa ya amince da hakan. Yanzu suna amfani da tsarin GIFMIS don samun ‘yanci wajen sarrafa kudinsu.

“Yadda gwamnati ke biyan albashi, daga ranar 25 ga wata ake fara biya. Wadanda ke kan IPPIS su ne ake bai wa fifiko. Kuma shi ya sa cikin watanni shida da suka gabata, inda nake jin ba dadi, ana biyan su ne a ranar 8 ko 9 ga wata mai zuwa.” kamar yadda ministan ya bayyana.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet