Featured
Kasafin 2026: Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 400 domin gina masallatai, gidajen sarakuna da ɗakunan taro
Kimanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 78 sun ware kusan Naira biliyan 400 a kasafin kudin 2026 domin gina da gyara dakunan taro, masallatai, fadojin sarakunan gargajiya, kasuwannin kauyuka da cibiyoyin al’umma.
Fiye da rabin kudaden an ware su ne ga ayyukan da ake ganin ba su da tasiri sosai wajen ci gaban kasa, ciki har da samar da hatsi, babura, keke Napep, tallafawa kungiyoyin ajiyar kudi, da gina gidajen tarihi da kananan filayen wasanni.
Rahoton da aka gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin hukumomin da ke cikin kasafin sun hada da Ma’aikatar Tsaro, Rundunar Sojin Sama, Nigerian Defence Academy da wasu hukumomin bincike. Sai dai masana sun ce irin wadannan ayyuka na iya karkatar da kudaden da ya kamata a mayar da su bangarori kamar lafiya, ilimi, tsaro, hanyoyi da wutar lantarki.
Wani masanin tattalin arziki, Chukwunonso Ihuma, ya zargi Majalisar Dokoki ta Kasa da rashin isasshen sa ido, yana cewa a wasu lokuta ‘yan majalisar na shigar da ayyukan da ba su da muhimmanci cikin kasafin. Ya kuma ce ya kamata a koma tsarin kasafin “zero budgeting”, inda za a sake tantance kowanne bangare daga tushe.
