Featured
Zaɓar Atiku a matsayin mataimakina shi ne babban kuskuren da na yi – Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce zaɓar Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 shi ne babban kuskuren da ya taɓa yi a lokacin da yake kan mulki. Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Charly Boy a wajen ƙaddamar da gidauniyarsa da littafinsa.
Obasanjo da Atiku sun samu rashin jituwa a wa’adin mulkinsu na biyu tsakanin 2003 zuwa 2007, lamarin da ya kai su ga shiga kotu tare da sukar juna. Sai dai daga baya sun sasanta, har Atiku ya ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, tsohon rikicin nasu ya sake kunno kai, inda Obasanjo ya zargi Atiku da bayar cin hanci ga marigayi Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na Abba. Atiku ya mayar da martani, yana zargin Obasanjo da nuna goyon baya ga Peter Obi yayin da yake ƙoƙarin share wa ɗan uwansa daga Kudu maso Yamma hanya.
Da yake amsa tambaya kan babban kuskurensa a mulki, Obasanjo ya ce da ya san Atiku yadda ya san shi daga baya, da bai zaɓe shi a matsayin mataimakinsa ba. Sai dai ya ce ayyukan Atiku da martaninsa ba su karkatar da hankalinsa daga abin da ya mayar da hankali a kai na Najeriya ba, yana mai cewa babu ƙiyayya a tsakaninsu.
