Featured
Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30, domin ’yan Najeriya su samu damar sayen man da farashi mai rahusa.
Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Read Also : Dangote Cement Obajana Awards Scholarships, Empowers Farmers, Market Women At Jakura Community
Oyedele ya ce za a yi rangwame kan farashin man fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko wajen cin gajiyar rangwamen.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi yarjejeniya kan farashin saukar da man fetur a tashar jiragen ruwa, inda za a rika duba farashin a kowane wata.
