Featured
Wasu daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu sun jefa ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali – Daniel Bwala
Mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar ya jefa wasu ƴan Najeriya cikin matsanancin talauci.
Sai dai Bwala ya ce duk da matsalolin da aka fuskanta, gwamnatin ta samu gagarumin ci gaba tun bayan fara aiwatar da sauye-sauyen. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels TV a shirin Politics Today.
Read Also : Waiya inaugurates Kano Intellectuals Forum, charges intellectuals to support socioeconomic development
Bwala ya ce ba abin mamaki ba ne samun matsin rayuwa yayin aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki, yana mai cewa gwamnati ta san cewa yawan mutanen da ke cikin talauci ya karu. Ya kuma ce gwamnati ta shafe shekaru uku tana bayyana wa ’yan Najeriya irin ci gaban da aka samu.
Dangane da zaɓen shugaban ƙasa na 2027, Bwala ya yi hasashen cewa Tinubu zai samu gagarumar nasara fiye da wadda ya samu a 2023, yana mai cewa tazarar da zai samu tsakaninsa da sauran ’yan takara za ta yi yawa matuƙa.

Pingback: Ba za mu amince a yi mana maguɗi a zaɓen 2027 ba - David Mark - KAKAKI 24