Featured
Babu gudu ba ja da baya kan batun cire tallafin man fetur – Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu gudu ba ja da baya kan batun komawa tsarin tallafin man fetur da aka cire, tana mai cewa dawo da tallafin zai iya kawo cikas ga sauye-sauyen da aka riga aka yi a ɓangaren man fetur. Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan yayin mayar da martani kan shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin idan ya lashe zaɓen 2027.
Onanuga ya bayyana alƙawarin Atiku a matsayin koma-baya ga Najeriya, kuma abu ne da ba zai dore ba ko an fara. A nasa ɓangaren, Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Read Also : Nan gaba hannun jarin matatar mu zai iya tashi daga 525 zuwa 10,000 – Dangote
Shugaba Tinubu ya kuma ce shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya nuna rashin fahimta kan harkokin mulki da tattalin arziki. Atiku ya ce dawo da tallafin na daga cikin muhimman manufofinsa na 2027, yana mai cewa cire tallafin bai samar da isasshen amfani ga ’yan Najeriya ba, musamman wajen rage tsadar rayuwa.
Sai dai masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa bai kamata muhawarar ta tsaya kan rage farashin man fetur kawai ba. Sun ce ya kamata a fi mayar da hankali kan yadda za a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati ta hanyar da za ta samar da ci gaba mai ɗorewa, ƙara samar da kayayyaki a cikin gida da kuma inganta rayuwar talakawa.
