Connect with us

Featured

Matatar Mai dake Kaduna zata fara aiki a watan Disamba

Karamin minista a ma’aikatar man fetur na tarayyar Najeriya Sanator Heineken Lok-pobiri ya ce, an fara daukar matakan farfado da ayyukan matatar man Kaduna, kuma akwai fatan cewa cikin watan Disambar shekara ta 2024, za ta dawo aiki gadan-gadan.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar aiki matatar ranar Asabar domin duba matsayin da aikin gyaran ke ciki.

Mutane sun fasa dakunan ajiyar kayayyaki na Majilisan Dinkin Duniya a Gaza

Karamin ministan wanda yake tare da babban shugaban gungun kamfanin mai na NNPC Malam Mele Kyari da sauran shugabannin kamfanin a yayin ziyarar, ya ce yana rangadin daukacin matatun man dake Najeriya ne a kokarin da gwamnati ke yi wajen tabbatar da ganin kafin wani lokaci mai tsawo Najeriya ta daina shigo da tattaccen mai daga waje kamar yadda shugaban kasa ya yi alkawari.

“Za mu yi duk abun da ya kamata wajen taimakawa kamfanin mai na NNPC domin ganin cewa mun biyawa ‘yan Najeriya burin su, gyaran matatun man yana da mahimmanci sosai ga dorewar tattalin arzikin mu.”

A lokacin da yake jawabi, babban shugaban gungun kamfanin mai na kasa Malam Mele kyari ya shaidawa ministan cewa, tuni kamfanin da zai yi kwangilar gyaran ya samar da dukkan kayayyakin aiki a matatar, kuma ma har ya fara aikin gyaran.

“Muna da yakinin cewa za mu sami kudaden da suka kamata wajen gudanar da wannan aiki har zuwa kammaluwar sa, wanda daga bisani zai kara sanya farin ciki a zukatan ‘yan Najeriya.”

Idan dai matatar man ta Kaduna ta fara aiki, ana sa ran za ta rinka tace ganga dubu 60 a kullum.

Sanata Heineken ya ce bisa la’akari da yadda aikin ke gudana, yana da kwarin gwiwar cewa matatar man ta Kaduna za ta iya dawowa aiki a wa’adin shekara guda da aka diba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet