Connect with us

Featured

Matsalar Da Gararambar Yara Ke Haifarwa A Cikin Al’umma

Haihuwar yara da wuya amma da dadi domin ga wasu da Allah ya baiwa ba don sun fi wanda bai bawa din ba, hasali ma wani lokacin wanda Allah ya hana Dan kan fi wanda ya baiwa iya kula da shi.

A kwana a tashi kuma yaran kan girma su zama iyaye sai dai Allah ya kawo mu wani zamani da yaran kan bar gaban iyayen su wasu da nufin neman ilimi wasu kuma sun rasa iyayen ne yayin da wasu Iyayen ne suka sallamawa duniya kamar yadda akan samu wasu yaran da dole ce take sanya su ficewa daga gida don nemowa iyayen abun da za a ci komai kankanatar wannan yaro.

A hannu gudu kuma yaran da ya kamata zu tafi makaranta sai kagansu a layi suna gararambar neman ina da shara da sassafe cikin unguwa.

Kwamaret A A Haruna Ayagi shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin Dan Adam na Kasa da Kasa ya yin tattanawarsa da wakilin Gidan Talabijin na Kakaki kan dalilin da yake sa yara gararamba a gari ya ce yaran nan suna yawo ne wuraren da zasu samu abinci domin duk inda yaro ya ke indai babu abinci to fa shi babu zaman lafiya komai zai iya yi.

Ya kara da cewa matsalar rabuwar aure tsakanin miji da mata tana janyo yaro ya rasa abubuwa da yawa domin kullum yana kan titin zuwa gidan Mahaifin ko mahaifiya wani lokacin ya fuskanci kora saboda bacin rai.

 

Kwamaret ya kuma ce tsana da azabrtarwar da matar Uba take yi wa yaran itama tana sanya su barin gidan su fantsama gari kamar yadda wasu Iyayen kan fake da Addini su turo kananan yara almajirci babu abinci kuma ba a baiwa malamin komai na kula da su ba.

Ya ce akwai yaran da ake samu basu ma san su wane iyayensu ba, idan an ci sa a ne ake samun masu sayar da kayayyaki a bakin danjar titi.

Ya ce mahukunta basa jaddada dokar da ta shafi yara, domin suma iyaye dole sai sun sa ido kuma doka ta yi aiki sannan za a samu saukin gararambar yara a tituna.

Ya ce matsalar nan babbace domin ana samun wadanda ake kawo su birni daga kauye domin aikatau.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet