Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mai Gari Da Wasu Mutane, Sun Hallaka Mutum Guda

Wasu ‘yan bindiga ne sun mamaye al’ummar garin Yashi da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara a karshen makon nan.

Ana zargin sun kashe mutum guda daya, suka kuma yi awon gaba da basaraken gargajiya a yankin, da wasu mutane 4.

‘Yan bindigar sun kuma hana mutanen yankin shiga gonakinsu, don haka ba za su iya girbe amfanin gona ba.

PDP Ta Zargi Gwamnan Nasarawa Da Yunkurin Bijirewa Umarnin Kotu

Honarabul Hamisu Alhaji Faru, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kan al’ummar a daren ranar Juma’a da misalin karfe 3 na dare.

Ya ce sun tafi da wani dan unguwar tare da wasu mutane 5 ciki har da sarkin gargajiya.

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro za su zage damtse wajen ganin an dakile ‘yan bindigar daga tafiya da wadanda aka sace.

Ya ce nan ba da dadewa ba za a ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma yi kira da a kwantar da hankula a cikin al’ummar yankin.

Ya kuma kara da cewa Gwamnan ya damu matuka da yanayin tsaro a jihar, kuma ba zai ja da baya ba wajen ganin an shawo kan matsalar ta tsaro.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet