Featured
Ƙungiyoyin Chelsea da Liverpool na farautar Mbappe
Ƙungiyoyin Chelsea da Liverpool da Manchester United da Newcastle United na farautar ɗan wasan Faransa da ke taka leda a PSG Kylian Mbappe, mai shekara 24.
A watan Janairun shekara mai kamawa kwantiraginsa zai ƙare, yayin da rahotanni ke cewa Real Madrid ba ta zawarcinsa.
A wani barin kuma Tottenham na farautar dan wasan gefe bayan da ta gano Micky Van de Van zai jima yana jinya, yanzu ɗan wasan Bournemouth Lloyd Kelly, mai shekara 25, take hari.
