Featured
Bayelsa: Babbar Jam’iyyar Hamayya Ta PDP Ta Gargadi Ganduje Kan Zuwa Rumfunan Zabe
Jam’iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta yi kakkausar suka kan ziyarar da shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, zai kai jihar kasa da sa’o’i 24 domin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar din nan.
Jam’iyyar PDP ta ce ziyarar za ta kara ta’azzara yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Sakataren yada labarai na PDP na jihar, Mista Ebiye Ogoli, ya ce jam’iyyar ta damu da yadda Ganduje ke shirin kai ziyara jihar a lokacin da INEC ta kayyade wa’adin yakin neman zaben jam’iyyun siyasa ya cika da tsakar daren ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwambar 2023.
Jam’iyyar PDP ta kuma bayyana cewa Shugaban jam’iyyar APC ba wani mai sa ido bane na kasa-da-kasa ko na cikin gida da aka amince da shi a zaben na ranar Asabar, kuma ba zai kada kuri’arsa a Bayelsa ba, kasancewarsa mai rijista a jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa kasancewar Ganduje a Bayelsa zai tabbatar da zargin cewa jam’iyyar APC ta kammala shirin yin magudi a zaben da kuma bayar da cin hanci a tsakanin masu zabe da kuma alkalan zabe.
Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, muna kira ga Shugaban jam’iyyar APC da ya fasa ziyarar da ya shirya kaiwa Bayelsa inji sanarwar.
