Featured
Muna Kira Ga Masoyanmu Su Cigaba Da Addu’a Don Samun Nasara A Kotun Koli – Gawuna
Ɗan takarar gwamnan Kano na jamiyyar APC da kotu ta ayyana nasararsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya buƙaci magoya bayansa da su ƙara dagewa da addu’a domin samun nasara a kotun ƙoli.
Gawuna ya faɗi haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayansa a Abuja.
Yayi godiya ga shugaban jamiyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda ya yi ƙoƙarin ganin sun samu nasara a kotu.
Nasiru Gawuna ya kuma yaba wa magoya bayan jam’iyyarsu ta APC bisa yadda suka jajirce.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar Kano bisa irin kyakykyawan zaton da suke yi masa.
