Featured
Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Soma Aiki A Gaza
Yarjejeniyar tsagaita musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki a yau Juma’a da misalin karfe 7 na safe agogon Gaza kamar yadda gwamnatin Qatar da ke shiga tsakani ta bayyana.
Tsagaita wutar za ta fara ne da zaran Hamas ta saki wasu Yahudawa da take garkuwa da su da suka haɗa da mata da ƙananan yara, kuma hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon makonni shida ana dauki-ba-dadi.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar, Dokta Majed al Ansari ya ce, sun karbi jerin sunayen mutanen da za a fara sakin su da misalin karfe 4 na Asuba a wannan Juma’ar, yayin da ake sa ran Isra’ila ita ma ta saki Falasdinawan da ta garkame a gidan yari.
