Featured
Shugaba Tinubu zai sasanta rikicin da ke tsakanin Gwamnan Ondo da Mataimakinsa
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani da nufin sasanta rikicin Gwamnan Ondo Oluwarotimi Akeredolu da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.
A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, wata majiya ta bayyana cewa shugaba Tinubu ya kira mambobin majalisar dokokin jihar Ondo domin su tattauna abyau Juma’a.
A makon da muke ciki ne manyan dattawa da sarakunan gargajiya suka roƙi shugaba Tinubu da ya sa baki a rikicin siyasar domin kaucewa barkewar yamutsi.
