Featured
Abdul Amart Mai Kwashewa Ya Siya Wa Iyalan Marigayi S Bono Gida
Mashiryin shirin fina-finan Kannywood Abdu Amart da aka fi sani da Maikwashewa ya siya wa iyalin Marigayi Director Aminu S Bono gida a unguwar Dandago kamar yadda mai bawa Gwamna shawara akan jinkai Fauziyya D Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook.
Tace “Abdul Amart ya sai musu gidan kusa da inda dangi da yan’uwan Aminu da mai dakinsa suke, yadda yan’uwa za su ci gaba da kula da iyalin nasa a kusa da su, yanzu Iyalan Marigayi Aminu za su taso daga can unguwar da suke domin dawowa gidan da aka sai musu.”
Muna addu’ar Allah ya saka wa Alh. Abdul Amart da alkairi, Allah ya duba zuri’arsa shima ko bayan baya raye.
