Featured
Abba K Yusuf Ya Naɗa Sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Harkokin Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Litinin din nan.
Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Bala mni ya yi a wannan wata na Nuwamba.
Dawakin-Tofa ya ce sabon Shugaban Ma’aikatan gogaggen ma’aikacin gwamnati ne wanda aka tabbatar da kwarewarsa a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin Kano daban-daban da ya yi aiki tsawon shekaru fiye da talatin.
