Connect with us

Featured

NUJ Freedom Radio ta taya ƙungiyar NAWOJ murna bisa nasarar zaɓen da suka samu

Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen Freedom Radio ta taya kwamrade Wasila Ibrahim Ladan murna, a matsayin sabuwar sakatariya ta Kungiyar ‘yan Jaridu mata ta kasa NAWOJ.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar kwamrade Aisha Muhammad Yalleman da kuma sa hannun sakataren kungiyar Kwamrade Muzamil Ibrahim Yakasai.

Ta cikin sanarwa, Kwamrade Aisha ta ce, Kwamrade Ladan ta cancanci matsayin da ta samu na sakatariya, sakamakon kwazonta da hangen nisanta akan ‘yan Jaridu mata a fadin Najeriya.

Sanarwa ta kuma ta ya Hajiya Aisha Ibrahim Bura murna a matsayin sabuwar shugabar kungiyar NAWOJ.

Kwamrade Aisha Yalleman ta yi fatan Hajiya Bura za ta hada kan ‘yan jarida mata na kasar nan, da nufin ciyar da kungiyar gaba, tare da fatan cewa, kungiyar za ta ci gaba da bai wa ‘yan jaridun horo akai akai ganin yadda aikin jarida a yanzu ke tafiya da zamani.

An dai gudanar da zaben kungiyar ta NAWOJ a ranar Asabar, Ashirin da biyar ga watan Nuwanban nan da muke ciki, a birnin tarraya Abuja.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet