Featured
Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Wurin Da Aka Kai Harin Bam A Kaduna
Babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ziyarci wurin da sojoji suka kai harin bama-bamai a unguwar Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar Talata.
Hafsan sojojin, da isarsa wurin, ya gana da Dangaladiman Zazzau da Hakimin Rigasa, Architect Aminu Idris, da sauran shugabanni da sauran al’umma.
Shugaban hafsan sojojin ya kuma ziyarci waɗanda abin ya shafa a Asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke Unguwar Rimi a cikin birnin Kaduna.
