Featured
Kotu ta yanke hukuncin rataya ga Sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami
Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zama a garin Potiskum, ta yanke wa korarren sojan, Las Kofur John Gabriel hukuncin rataya ne a ranar Talata.
Alkalin kotun, Usman Zanna Mohammed, ya kuma yanke wa abokin lafinsa, Las Kofur Adamu Gideon, hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari.
Mai shari’a Usman Zanna Mohammed ya yanke wa Gabriel hukuncin ne karkashin dokar soja.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Mohammed ya ce bayan yin nazari sosai kan hujjojin da ke gaban kotun da kuma yadda wadanda ake tuhumar suka kasa bayar da wasu muhimman shaidu da za su tabbatar da da’awarsu, ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin da ya dace da su.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun kashe Sheikh Goni Aisami ne a Karamar Hukumar Karasuwa ta jihar Yobe, a kokarinsu na kwace motar malamin, a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Gashua daga Kano a ranar 22 ga watan Agustan 2022.
