Featured
Kano: Hayaniya ta kaure a Majalisa kan kuɗaɗen Masarautu
An tayar da jijiyoyin wuya a zauren Majalisar Dokokin Kano, kan kudaden da gwamnatin jihar ta ware wa masarautu a karamin kasafinta na 2023.
Takaddamar ta kaure ne a yayin zaman tantance kwarya-kwaryan kasafin kudi na Naira biliyan 24 da Gwamna Abba Kabir ya gabatar domin amincewar majalisar.
yayin bibiyan kasafin ne ’yan majalisa suka diga alamar tambaya bayan da suak ga an ware masarautan Kano, Gaya, Rano da Bichi Naira miliyan 2.5 kowannensu, amma aka ware wa Masarautar Karaye Naira miliyan 50 a cikin kasafin.
A yayin hayaniyar ne shuugaban majalisar, Jibrin Falgore, ya bayyana wa mambobi cewa Masarautar Karaye ce kadai ta kare kasafin da aka ware mata a cikin masarautu biyar da ke jihar.
Bayan bayanin da shugaban majalisar ya yi musu ne kurar ta lafa.
A karshen zaman dai, Majalisar ta amince da karamin kasafin kudin na karin Naira biliyan 24 a kan kasafin jihar na shekarar 2023.
Amincewar majalisar da kwarya-kwaryan kasafin da Gwamnan ya gabatar mata ya kara yawan kasafin jihar na 2023 zuwa biliyan 350.
