Featured
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daraktan Cibiyar Bincike Na Jami’ar Tarayya Dake Gusau
Wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani daraktan Cibiyar Bincike na Jami’ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, Bello Janbako.
Janbako, wanda kuma babban malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar, an yi garkuwa da shi a gidansa da ke Damba a Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba.
Wani mazaunin yankin mai suna Nasamu Garba ya shaidawa majiyarmu cewa ‘yan bindigar sun shiga gidan Janbako ne da misalin karfe 2 na daren Larabar inda suka tafi da shi.
Garba ya ce jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindigar a yunkurinsu na dakile sace malamin.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an sace wani mazaunin yankin wanda darakta ne a ma’aikatar kudi ta jihar Malam Sabiu kwanaki biyu da suka gabata.
