Featured
TUC tace gwamnatin tarayya ta gaggauta saka sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata
Ƙungiyar Kwadago ta TUC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saka sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya domin magance tsadar rayuwa a kasar.
BBC ta ruwaito cewa tun bayan cire tallafin man fetur, tsadar rayuwa ta yi kamari sannan kuma an samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
Duk da cewa an gudanar da zanga-zanga da tarurruka tsakanin kungiyoyin kwadago da hukumomi domin fitar da matakan sassauta wahalhalun da ake fama da su, shugaban TUC, Festus Osifo ya yi kira da a sake duba mafi karancin albashi na N30,000.
Ya yi wannan magana ne a Abuja ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai sa’o’i 24 kafin fara zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gudanar a fadin kasar kan tsadar rayuwa.
Osifo ya shaida wa mahalarta taron cewa kiran da aka yi na neman sabon mafi karancin albashi na daga cikin hanyoyin da ƙungiyar ta fitar domin magance taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar.
Ya ce faduwar darajar Naira a kan dala a kasuwannin canji ya kara dagula darajar mafi ƙarancin albashi.
Don haka shugabannin TUC suna yin kira da a amince da aiwatar da sabuwar dokar mafi karancin albashi da zai yi daidai da yanayin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
A cewarsa, ya kamata tawagar gwamnatin ƙasar a fannin tattalin arziki ta yi kokarin ganin an samu daidaiton darajar Naira zuwa dala, wanda suka sanya tsakanin dala ɗaya kan naira 500 zuwa 800.
Osifo ya kuma ba da shawarar cewa ya kamata gwamnati ta sake duba haraji kan wasu muhimman kayayyaki da ake shigo da su cikin ƙasar domin a samu sauƙin wahalhalun da ake ciki.
Shugaban na TUC ya dora alhakin rashin tsaro ne da ya jawo tashin farashin kayan masarufi a halin yanzu, inda ya ce manoma da dama ba su zuwa gonakinsu ta dalilin hakan.
