Featured
Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta A Turereniyar Sayan Shinkafa
Mutane bakwai, ciki har da mace mai juna biyu sun rasu a yayin turereniyar sayen shinkafar da Hukumar Kwastam ta yi gwanjo a kan N10,000 kowane ƙaramin buhu a Jihar Legas.
Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da ke gwajon shinkafar da karfin tuwo.
Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba.
Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani bangare na yunkurinta rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da ake fama da ita fadin kasar.
