Featured
BUK Za Ta Karrama Sanata Barau Da Digirin Girmamawa
Jami’ar Bayero Kano za ta karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina da digirin girmamawa, duba da irin gudunmawar da suka bayar a fannin ilimi da ci gaban matasa.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba wa shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce, za a yi bikin ne a ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2024, yayin bikin yaye daliban jami’ar karo na 38 a sabuwar jami’ar da ke kan titin Gwarzo.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce, “Hukumar jami’ar ce ta amince da wannan kudirin na karrama su da digirin girmamawa”
