Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Jero Jihohi 14 Da Makarantunsu Suke Cikin Hadari
Gwamnatin tarayya ta bayyana wasu jihohi 14 da makarantun su ke cikin hadari, dai-dai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kutsawa makarantu suna garkuwa da dalibai.
Shugabar hukumar kula da makarantu ta kasa Hajiya Halima Iliya ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.
Halima ta bayyana cewa jihohin sun hadar da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, birnin tarayya Abuja, Kebbi, Sokoto, Plateau, Zamfara da karin wasu guda 3.
Bayanin hukumar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da yara kusan 300 a jihar Kaduna, cikin su guda 28 sun tsere.
Kwana guda a tsakani kuma wasu ‘yan bindigar suka sace daliban tsangaya 15 a jihar Sokoto.
