Addini
Mun Kammala Kashi 70 Bisa 100 Na Shirye-Shorten Aikin Hajjin Bana – NAHCON
Hukumar Jin dadin alhazai ta KAsa NAHCON, ta ce shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2024 ya kai kusan kashi 70 cikin 100.
Shugaban Hukumar, Alhaji Jalal Ahmad-Arabi, ya shaida wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi, cewa hukumar za ta tabbatar da an gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa Ahmad-Arabi ya je jihar ne domin wani rangadi a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello International Airport da kuma sansanin Aikin Hajjin jihar Kebbi.
Ziyarar dai ita ce ta tabbatar da dacewa filin jirgin ya kasance daya daga cikin cibiyoyin jigilar alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajjin na bana.
