Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Shawarar Hukuncin Kisa Kan Masu Barnata Kayan Wutar Lantarki
Gwamnatin tarayya ta bada shawarar zartar da hukuncin kisa kan masu barnatar sa kayayyakin wutar lantar da barayi.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ba da shawarar hukuncin me ga masu barnata Mayan wutar lantarki da masu sata.
Ministan ya bukaci haka ne a Abuja yayin da yake mayar da martani kan barnatar da kayan wutar lantarki da ake yawan yi.
Adebayo ya ce batun barna da satar kayan wutar lantarkin na daya daga cikin matsalolin da bangaren ke fuskanta a halin yanzu.
Ministan ya ce ma’aikatar tana hada kai da gwanatocin jihohi don samun tsarin da zai kare ababen more rayuwa.
