Featured
Ƴanbindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 14 a kauyen Dogon Noma-Ungwan Gamo da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Lamarin ya zo ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da mutane 61 a yankin Buda da ke karamar hukumar Kajuru.
Hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da harin ba. Sai dai wani shugaban matasa Sani Musa ya shaidawa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar da suka kai hari a ranar Asabar din da ta gabata a yankin Dogon Noma suna da yawa.
Ya ce Sun fara harbe-harben kan mai Uwa da wabi, inda suka yi awon gaba da mutane goma sha hudu yayin da mutum daya ya samu rauni.
A cewar shugaban matasan, wanda ya samu rauni, Jibrin Dauda, an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
